
Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama a ƙasa mai tsarki sakamakon yawaitar Hausawa ko dai ƴan safara ko kuma masu Ibada koma mazauna wannan ƙasar ta Saudiyya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Audio and video play straight from the show's own hosting. PodSubs stores and serves no media.

