
Yadda gwamnan Bauchi ya dakatar da Mai Martaba Sarkin Lame
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' zai duba yadda mahukunta a jihar Bauchi suka dakatar da Mai Martaba Sarkin Lame. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar, Mai Martaba Alhaji Aliyu Yakubu Lame, daga jagorantar harkokin masarautar bisa zargin aikata ba daidai ba. Gwamnan ya kuma amince da kafa kwamitin mai mambobi 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken, inda aka ba kwamitin wa’adin makonni uku domin gabatar da rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati. Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama, da kuma rahotannin sirri daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro kan zargin amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, yin amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba da sauran halaye da ake ganin sun saɓa da nauyin da ke kan mai sarautar gargajiya.
Audio and video play straight from the show's own hosting. PodSubs stores and serves no media.

