
Rawar da tawagogin Najeriya suka taka a wasannin neman shiga AFCON da Olympic
Shirin a wannan makon zayyi duba ne kan wasanni sharen fagen zuwa gasar lashe kofin nahiyar Afrka ta AFCON da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tsakaninta da Tanzania, bayaga wanda itama tawagar ƴan ƙasa da shekaru 23 da aka fi sani da Olympics Eagles ta yi da takwararta ta DRC. Bayaga tawagar Super Eagles, ita dai ƙanwarta ta ƴan ƙasa da shekaru 23 wato Olympics Eagles, ta buga nata wasannin neman gurbin tsakaninta da takwararta ta DRC, inda wasan farko tasha kashi da ci 2 da nema, amma a wasa na biyu da ya gudana a filin wasa na Remon Stars da ke garin Ikenne a jihar Ogun, Najeriyar ce ta maida biki ta hanyar lallasa DRC da ci 4 da nema, wani al’amari da ya bata damar tsallakawa zagaye na gaba inda za su ƙara da Zambia, a wasannin neman gurbin zuwa gasar AFCON ta wannan mataki, haɗi da neman gurbin zuwa gasar Olympics da za a yi a shekarar 2028.
Audio and video play straight from the show's own hosting. PodSubs stores and serves no media.

